Dangote ya ƙaddamar da aikin gina kamfanin takin zamani na dala biliyan 2.5 a Habasha

0
1000200555
Spread the love

Rukunin kamfanoni na Dangote ya ƙaddamar da fara aikin gina kamfanin takin zamani na Dangote Gode Fertilizer a ƙasar Habasha.

Shugaban rukunin kamfanonin, Alhaji Aliko Dangote ne ya jagoranci ƙaddamar da fara aikin gina kamfanin mai suna Dangote Gode Fertiliser Plant wanda za a garin Gode da ke ƙasar Habasha.

Daga cikin waɗanda suka samu halartar ƙaddamar da fara aikin, akwai Firaministan Habasha, Abiy Ahmed da shugaban kamfanin man fetur na MRS, Sayyu Dantata da shugaban rukunin kamfanonin NGX, Umaru Kwairanga da shugaban kamfanin hannun zuba jari na Habasha, Biru Taye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *