Iran ta kashe mutum shida masu alaƙa da Isra’ila

Rahotanni na nuna cewa hukumomi a Iran sun ce an kashe wasu mutane shida da aka samu da laifin ta’addanci da alaka da Isra’ila.
Ma’aikatar shari’a ta kasar ta ce mutanen mambobi ne na wata kungiyar ‘yan ta’adda ta ‘yan aware da suka yi ikirarin kashe jami’an tsaro hudu tare da kai harin bam a lardin Khuzestan da ke yammacin kasar.
Mahukunta sun ce an dauki matakin ne bayan cika dukkan ka’idojin shari’a.
Iran da Isra’ila sun gwabza yaki na tsawon kwanaki goma sha biyu a watan Yuni.
