Kungiyoyin sa ido kan rashawa sun zargi Wike da boye kadarori

0
1000196616
Spread the love

Gamayyar ƙungiyoyin da ke sa ido kan shugabanci na gari da cin hanci da rashawa, sun yi kiran a gaggauta gudanar da bincike kan ministan babban birnin Tarayya Abuja Nyesom Wike, kan zarge-zargen boye kadarorinsa da kin bayyana su wanda hakan ya saba wa dokokin Najeriya.

A cikin sanarwar hadin gwiwa da suka fitar, sun yi kira ga hukumomin binciken cin hanci da rashawa da suka hada da EFCC da ICPC da CCB da NJC da hukumar haraji ta FIRS su dauki matakin gaggawa kan Wike.

Sanarwar ta ci gaba da cewa babu wani jami’in gwamnati komai mukaminsa da ya fi karfin hukuma, sun ce hakan na janyo ƙimar Najeriya na raguwa a idon duniya.

Sun kara da cewa, akwai kwarararn rahotanni da ke alakanta ministan da maidakin shi Mai shari’a Eberechi Suzzette Nyesom-Wike ta kotun daukaka kara da tarin kadarorin da ba su bayyana kamar yadda doka ta tanada ga duk mai rike da madafun iko.

Ciki har da manyan dogayen gine-gine masu daraja har 3 a jihar Florida ta Amurka da aka siya a shekarar 2021 zuwa 2023, ana kuma zargin sun sayawa ‘ya’yansu ne.

Harwayau, da wasu gidajen alfarma da manyan motoci da suka mallaka amma da sunan wasu ‘yan uwansu a Abuja.

Gamayyar kungiyoyin sun kuma yi wani zargin na karkatar da dala miliyan 300 na gyara muhalli a Ogoni da malalar mai ya lalata da suma aka karkatar ga kamfanoni masu zaman kan su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *