Mako mai zuwa jirgin ƙasan Abuja – Kaduna zai koma aiki

Hukumar jirgin ƙasa ta Najeriya NRC ta ce ta kammala gyare-gyare a hanyar dogon Abuja-Kaduna, inda ta ce jirgin zai koma aikin jigilar fasinja a hanyar a mako zuwa.
A ranar 26 ga watan Agusta ne dai jirgin ya tuntsure, inda wasu mutane da dama suka samu raunuka, lamarin da ya sa aka dakatar da aikin jirgin domin a yi gyara.
A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Callistus Unyimadu ya fitar, ya ce hukumar ta yi aiki tuƙuru wajen tabbatar da kammala gyare-gyaren cikin tsanaki.
“A ƙoƙarinmu na inganta jin daɗi da walwalar fasinja, NRC ta mayar wa fasinja 512 kuɗin tikitin fasinjojin da suke cikin jirgin da ya tuntsure. Sannan muna shirye-shiryen mayar da kuɗin sauran fasinjojin suma domin tabbatar da kowa ya karɓi kuɗinsa.”
Sai dai sanarwar ba ta bayyana asalin ranar da jirgin zai koma aiki ba, inda ya ce, “nan da kwanaki kaɗan za mu bayyana asalin ranar da za mu fara jigila, da kuma tsare-tsarenmu.”
