Gomman wakilai sun fice daga taron MDD yayin da Netanyahu zai fara jawabi

0
1000184285
Spread the love

Gomman jami’an Diplomasiyya ne suka yi ta tururuwar ficewa daga babban zauren majalisar Dinkin Duniya yayin da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu zai fara gabatar da jawabinsa.

Babban ɓangare na zauren ya kasance fayau yayin da Netanyahu ke gabatar da jawabin nasa, a daidai lokacin kuma masu zanga-zangar adawa da yaƙin Gaza suka taru a dandalin Times, kusa da wurin da ake taron.

Yayin da jawabin nasa Netanyahu ya soki wakilan ƙasashen musamman na Yamma da suka amince da kafuwar ƙasar Falasɗinu.

Netanyahu ya bayyana matakin amincewar a matsayin ”alamar abin kunya”, da ya ce yana aika saƙon cewa ”kisan Yahudawa na da riba”.

Isra’ila ta fuskanci matsalin lamba daga ƙasashen duniya kan matakin soji da ta ɗauka kan Gaza, lamarin da ya sa Birtaniya da Faransa da Kanada da Australiya da wasu ƙasashen suka amince da kafuwar ƙasar Falasɗinu a wannan mako.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *