Sama da kashi 90 sun amince da gyaran ƙundin tsarin mulki a Guinea

0
1000176718
Spread the love

Fiye da kashi 90% na ƴan ƙasar Guinea sun amince da gyaran ƙundin tsarin mulki a zaɓen raba gardama da aka gudanar ranar Lahadi, kamar yadda sakamakon farko ya nuna a daren Litinin.

Ana ganin wannan zaɓen mataki ne na dawo da mulkin farar hula.

Duk da haka, sabon tsarin mulkin zai ba Janar Mamady Doumbouya damar yin takara a zaben shugaban ƙasa kuma ya tsawaita wa’adin mulkinsa daga shekaru 5 zuwa 7.

Shugabannin jam’iyyu biyu masu adawa da suka haɗa da Cellou Dalein Diallo da tsohon shugaban ƙasar Alpha Condé, sun yi kira ga mutane da su yi watsi da zaɓen.

A halin yanzu dai an dakatar da jam’iyyunsu.

Masu sukar gwamnati sun ce zaɓen yunƙuri ne na kama iko, yayin da ƙungiyar kare haƙƙn bil’adama ta Human Rights Watch ta zargi gwamnati da dakatar da jam’iyyun adawa da kuma rufe kafafen yaɗa labarai.

A makonni kafin zaɓen, rundunar soji ta dakatar da jam’iyyu uku da rushe fiye da jam’iyyun siyasa 50.

Kimanin mutum miliyan 6.7 ne suka yi rajista don kada kuri’a a ƙasar. Ana sa ran gudanar da zaben shugaban ƙasa kafin ƙarshen shekara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *