Museveni zai sake tsayawa takarar shugaban Uganda bayan shekara 40 a mulki

Hukumar zaɓen ƙasar Uganda ta amincewa shugaba ƙasar mai shekaru 81, Yoweri Museveni, wanda ya riƙe mulkin ƙasar kusan shekaru arba’in, ya tsaya takarar shugabancin ƙasar a zaben da za a gudanar shekara mai zuwa.
A jawabin amincewarsa, Museveni ya yaba wa jam’iyyarsa kan zaɓen sa a matsayin wanda zai tsaya takara.Museveni yana neman wa’adi na bakwai a shugabancin ƙasar.
Ana sa ran zai yi magana ga magoya bayansa a wani taron jama’a a filin ‘Independence Grounds’ kusa da Kampala.Za a tsayar da babban abokin hamayyarsa, Bobi Wine a gobe.
Jam’iyyu hudu sun riga sun fice daga takarar, ciki har da jam’iyyar Democratic da jam’iyyar PFF ta Dr. Kizza Besigye.
Besigye, wanda aka kama a Kenya a shekarar da ta gabata kan zargin cin amanar ƙasa, ba zai bayyana a takardar zabe ba.Masu sukar gwamnati na cewa Museveni ya mulki Uganda da karfi tun 1986.
A zaben 2021, ya samu kashi 58 yayin da Bobi Wine ya zo na biyu da kashi 34 Ana sa ran gudanar da zaɓen a ranar 12 ga Janairu a shekara mai zuwa.
