Falasɗinu ta buƙaci sauran ƙasashe su amince da ƙasar Falasɗinu

Shugaban Falasdinawa ya yi kira da a samu karin wasu kasashe da za su bi bayan Faransa da Birtaniya wajen amincewa da Falasɗinu a matsayin kasa.
Shugaban Falasɗinawan ya cewa “mun yaba wa matsayin ƙasashen da suka amince da Falasɗinu a matsayin kasa, sannan kuma muna kira ga wadanda ba su bayyana matsayarsu ba da su bi sahun wadannan kasashe.
“Mahmud Abbas, ya kuma jinjina wa shugaban Faransa Emmanuel Macron, a taron Majalisar Dinkin Duniya cewa duk wata hanyar samun zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya ta dogara ne wajen samar da kasashe biyu masu ‘yanci.
Ana kyautata tsammanin shugaba Trump zai mayar da martani akan wannan mataki na wadanann ƙasashe a ganawar da zai yi da shugabannin kasashen Larabawa da kuma jagororin addinin musulunci a New York.
