Hisbah ta daƙile yunƙurin safarar wasu mata daga Kano zuwa ƙasashen waje

0
1000174653
Spread the love

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce jami’anta sun yi nasarar daƙile wani shirin safarar mata huɗu daga Kano zuwa wasu kasashe domin neman kuɗi inda ta ce ta dauki matakin gaggawa domin hana aukuwar lamarin.

Hukumar ta bayyana cewa an yaudari matan ne da cewa za su samu takardun izinin tafiya da biza a Ghana, sannan daga nan za su tafi Saudiyya domin samun ayyukan yi.

Hukumar ta kuma ce ta tabbatar da cewa, an tsare lafiyarsu, domin karesu daga faɗawa cikin haɗarin cin zarafi ko bautar da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *