Kasashen Afirka 52 cikin 54 sun amince da Falasɗinu a matsayin ƴantacciyar ƙasa

0
1000174643
Spread the love

A yayin da Birtaniya, Australia da kuma Canada suka bi sabun sauran ƙasashen duniya sama da 140 domin amincewa da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai ƴanci, a nahiyar Afirka kuwa, yanzu haka ƙasashe 52 daga cikin 54 ne suka amince da wannan ƴanci.

Mafi yawan ƙasashen nahiyar Afirka sun amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa ne kimanin shekaru 37 da suka gabata, inda kawo yanzu adadinsu ya kai 52 daga cikin 54, ma’ana dai ƙasashen Kamaru da Eritrea ne kawai suke ware kansu a game da wannan batu.

A ranar 15 ga watan Nuwambar 1988 ne Yasser Arafat jagoran gwagwarmayar Falasɗinu ya shelanta ƴancin yankin a lokacin wani taro da ya gudana a birnin Algers na Aljeriya, inda a wannan rana Aljeriya ta kasance ƙasa ta farko a duniya da ta amince da ƴanci Falasɗinu.

Nan take kuma sai ƙasashen Moroko, Tunisia da kuma Mauritania suka amince da hakan, yayin da a cikin makonni kaɗan aka samu ƙasashen duniya 75 da suka amince da kafuwar ƙasar, kuma mafi yawansu daga Afirka Yankin Kudu da Sahara ne irinsu Sudan, Najeriya, Burkina Faso, Senegal da kuma Guinea.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *