Isra’ila ta soki masu amincewa da ƙasar Falasɗinu

Ma’aikatar harkokin wajen Isra’ila ta bayyana amincewa da ƙasar Falasɗinu a matsayin “saka wa ƙungiyar Hamas – wadda ke samun ƙwarin gwiwa daga Musulman Birtaniya”.
Cikin wani saƙo a dandalin X, ma’aikatar ta soki matakin na Birtaniya da Canada da Australia da suka sanar a yau Lahadi.
“Shugabannin Hamas sun sha bayyanawa cewa wannan amincewar sakamako ne kai-tsaye na harin ranar 7 ga watan Oktoba,” in ji sanarwar.
