Sojojin Najeriya sun ce sun kashe mayaƙa 15 a jihohin Yobe da Borno

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce jami’anta sun kashe mayaƙa sama da 25 a wasu hare-hare da suka kai a yankin Bula na jihar Yobe da Banki na jihar Borno.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, Ehimen Ejodame ya fitar a ranar Asabar.
A cewarsa, sojojin na Najeriya sun kai farmakin ne haɗin gwiwa a ranar 18 ga watan Satumba bayan samun bayanan sirri.
Ya ce hakan ya sa suka yi amfani da fasahar zamani wajen ganowa da tattara bayanan zirga-zirgar mayaƙan, sannan suka far musu.
“Sojojin Najeriya sun samu nasarar kashe aƙalla ƴanta’adda guda 25 a wani farmakin haɗin gwiwa a yankin Bula na jihar Yobe da yankin Banki na jihar Borno a ranar 18 ga Satumba,” in ji shi.
