Canada ta amince da ƙasar Falasɗinu

Firaministan Canada Mark Carney ya ce daga yau (Lahadi) “Canada ta amince da ƙasar Falasɗinu” a hukumance.
Cikin wata sanarwa da ya wallafa a dandalin X, Mista Carney ya ce:
“Canada ta amince da ƙasar Falasɗinu kuma muna miƙo tayinmu na taimakawa wajen samar da zaman lafiya tsakanin Falasɗinawa da Isra’ila.”
