Mutum ɗaya ya mutu a fashewar da aka samu a Kamafanin Kera Makamai da ke Kaduna

0
1000171220
Spread the love

Wata fashewa da aka samu a Kamafanin Kera Makamai ta Najeriya DICON da ke Kaduna, ya yi sanadin mutuwar mutum guda tare da jikkata wasu da dama.

Rahotanni sun nuna cewa fashewar ta faru ne a lokacin da ake ƙoƙarin zubar da lalatatciyar hodar haɗa harsasai a cibiyar hukumar da ke Kurmin Gwari da ke Unguwar Kakuri ta ƙaramar hukumar Kaduna ta Kudu.

A cewar sanarwa mai ɗauke da sa hannun jami’ar hulɗa da jama’a na kamfanin Maria Sambo, ta ce mutum ɗaya ya mutu a hatsarin, yayin da wasu da dama suka samu raunuka.

Ta ce yanzu haka an garzaya da waɗanda suka samu raunuka Asibitin Sojoji na 44 da ke cikin garin Kaduna, don samun kulawar da ta kamata.

Shaidun ganin da ido sun ce fashewar ta yi sanadiyar fashewar gilasan gidajen da dama da ke makwabtaka da wurin, wanda suka bayyana a matsayin mai ban tsoro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *