Hatsarin kwale-kwale ya halaka mutanen da ke gujewa harin ƴan bindiga a Sokoto

Wani hatsarin kwale-kwale ya laƙume rayukan mutane da dama a jihar sokoto da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya, yankin da ke fama da tashe-tashen hankula sakamakon ayyukan ƴan bindiga.
Lamarin ya faru ne daidai lokacin wasu mazauna garin Zalla Bango, wani ƙaramin ƙauye a yankin ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto, ke ƙoƙarin tserewa zuwa wasu yankunan ƙasar domin tsira daga hare-haren ƴan bindiga da ke ƙara ta’azzara a yankin.
Wasu bayanai daga yankin sun ce, mafi yawan waɗanda lamarin ya rutsa da su mata ne da ke ƙoƙarin tsallaka ruwa zuwa wasu yankunan, a wani yunƙuri na tserewa hare-haren da ƴan bindiga ɗauke da makamai ke kai wa yankinsu.
Bayanan sun ƙara da cewa, hatsarin ya faru ne daidai lokacin da jirgin ruwan da ke kan hanyar Goronyo zuwa Sabon Birni ɗauke da fasinjojin ya bugi gefen wata magudanar ruwa da ta ruguje, lamarin da ya haifar da kifewar jirgin inda nan take ya nutse a ruwan.
Tuni dai, shugaban ƙaramar hukumar ta Sabon Birni Alhaji Ayuba Hashimu, ya tabbatar da aukuwar lamarin, sai daihar kawo yanzu ba a tabbatar da adadin waɗanda suka mutu a hatsarin ba.
