Ambaliya ta kashe mutum uku a jihar Adamawa – NEMA

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya ta ce ambaliyar ruwa ta kashe mutum uku a jihar Adamawa da ke arewacin ƙasar.
Wata sanarwa da National Emergency Management Agency (Nema) ta fitar ranar Alhamis ta ce aƙalla mutum 1,415 ne ambaliyar ta shafa bayan ruwan sama mai ƙarfi tun daga ranar Talata.
Ta ce an zabga ruwan ne a yankunan Yola ta Arewa da Yola ta Kudu, inda fiye da mutum 40 suka ji raunuka sannan ruwan ya rusa gidaje da kuma shafe gonaki da dama.
Jimilar unguwanni 13 lamarin ya shafa, in ji Nema.
