Indiya ta tuhumi ‘yan Najeriya 106 da safarar miyagun ƙwayoyi a 2024

0
1000170297
Spread the love

Hukumomi a Indiya sun tuhumi ‘yan Najeriya 106 da laifin safarar miyagun ƙwayoyi a shekarar 2024 da ta gabata, kamar yadda jaridar Indian Express ta ruwaito.

Rahoton ya ce ‘yan Najeriyar na cikin jimillar mutum 660 ne da rahoton shekara na hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi ya bayyana tare wasu daga ƙasashen Nepal (203), da Myanmar (25), waɗanda su ne suka fi yawa a jerin.

Kazalika, akwai ‘yan Bangladesh (18), da Ivory Coast (14), da Ghana (13), da Iceland (10) waɗanda aka tuhuma da laifukan ta’ammali da ƙwayoyi.

“Indiya na fama sosai wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi saboda faɗin ƙasa da take da shi,” a cewar Ministan Harkokin Cikin Gida Amit Shah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *