Najeriya ta ci alwashin hukunta Qatar Airways kan wahalar da fasinja

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya ta ci alwashin ɗaukar matakin ladaftarwa kan kamfanin jirgin Qatar Airways saboda zargin sa da “wahalar” da fasinjan ƙasar.
Nigerian Civil Aviation Authority (NCAA) ta faɗa cikin wata sanarwa ranar Juma’a cewa kamfanin bai bi ƙa’idojin kare haƙƙin fasinjoji ba na hukumar bayan wata ma’aikaciyar jirgin ta zargi wani fasinja da cin zarafi ta hanyar taɓa bayanta.
“Qatar Airways bai kawo wa NCAA rahoton fasinjan ba, har sai da suka sauka a birnin Doha na Qatar sannan aka tsare shi kusan awa 18, aka ci tarar sa, sannan aka tilasta masa saka hannu kan wata yarjejeniya da Larabci,” in ji kakakin NCAA Michael Achimugu cikin wani saƙo a dandalin X.
Kazalika, “an tilasta wa fasinjan sayen wani tikitin domin ƙarasawa Amurka bayan Qatar Airways ya ƙi amincewa ya kai shi”. Jirgin ya tashi ne daga Legas zuwa Amurka bayan ya yi zango a Doha.
Achimugu ya ce da ma kamfanin ya sha nuna rashin ɗa’a ga hukumar a baya, “abin da ya sa dole ne a dakatar da wannan ɗabi’ar a yanzu”.
