Babu abin da mahaifina ya tsinana wa Kamaru sai wahala – Brenda Biya

Ƴargidan shugaban Kamaru, ta yi kira ga ƴan ƙasar kada su sake zaɓar mahaifinta a zaɓen shugaban ƙasar da ke tafe cikin watan Octoban.
Cikin wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na TikTok, Brenda Biya ta ce babu abin da mahaifinta ya tsinana wa mutanen Kamaru ciki har da danginta sai wahala.
A shekarar da ta gabata ne Brenda Biya ta fito ƙarara ta bayyana cewa ita ƴar maɗigo ce, wanda kuma hakan babban laifi ne a ƙasar da ke tsakiyar Afirka.
Ana sa ran Paul Biya – shugaban ƙasar da ya fi kowa daɗewa kan karagar mulki a duniya – zai lashe zaɓen shugaban ƙasar da za a yi cikin watan Octoba, a wa’adin mulki na 12, bayan da aka haramta wa babban mai hamayya da shi, Maurice Kamto.
