Shugaban Falasɗinawa zai yi jawabi a taron MDD ta bidiyo

0
1000103636
Spread the love

Shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas zai yi jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya ta bidiyo a mako mai zuwa bayan da Amurka ta hana shi bizar shiga birnin New York.

Mambobin Majalisar sun amince da kudirin da zai bai wa Mista Abbas damar yin jawabi a wurin taron shugabannin kasashen duniyar.

A watan da ya gabata, Amurka ta ce ta hana Mr Abbas da wasu jami’an Falasdinawa 80 takardar bizar saboda kokarin da suke yi na ganin wasu kasashe sun amince da kafa kasar Falasdinu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *