‘Amurka na shirin sayar wa Isra’ila makamai na dala biliyan shida’

0
1000046958
Spread the love

Kafafen yaɗa labaran Amurka sun bayar da rahoton cewa gwamnatin Trump na neman amincewar majalisar dokokin ƙasar don sayar wa Isra’ila kayan aikin soji na kusan dala biliyan shida.

An fahimci shirin ya ƙunshi jirage masu saukar ungulu 30 masu kai hari, da kuma motocin yaƙi fiye da 3,000.

Labarin shirin sayar da makaman na zuwa ne yayin da Isra’ila ta sanar da fara ƙaddamar da abin da ta kira ƙarfin da ba ta taɓa amfani da shi ba a ci gaba da hare-haren da take kai wa Birnin Gaza.

A ranar Juma’a rundunar sojin Isra’ila ta ce kusan Falasɗinawa 480,000 ne suka bar birnin tun ƙarshen watan Agusta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *