Saudiyya ta saki ƴan Najeriya da aka zarga da safarar muyagun ƙwayoyi

Hukumomin Saudi Arabia sun saki wasu ƴan Najeriya uku da aka tsare a Jidda, bayan an zarge su da safarar miyagun ƙwayoyi
Mutanen da aka saka su ne Maryam Hussain Abdullahi da Abdullahi Bahijja Aminu da Abdulhamid Saddieq.
Wasu gungun mutane da ke aiki a filin jiragen sama na ƙasa da ƙasa na Mallam Aminu da ke Kano (MAKIA) ake zargi da manna sunayen mutanen uku a wasu akwatuna da ke ƙunshe da muyagun ƙwayoyin.
Hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ce ta sanar wa manema labarai batun sakin mutanen uku.
Unda ta ƙara da cewa mutanen uku ce sun ɗauki akwatunan miyagun kwayoyin sun shiga jirgin Ethiopian Airline ET940 da ya bar Kano zuwa Jidda a ranar 6 ga watan Agusta, 2025, domun yun umara.
Kuma bayan isarsu Jidda ne aka kama su.
Binciken da aka yi ya kai ga kama wani mai shekara 55 Mohammed Ali Abubakar da aka fi sani da Bello Karama, wanda shi ne jagoran waɗanda ake zargi da musanya akwatunan da wasu mutum uku, ciki har da ma’aikacin jirgin.
Tuni aka gabatar da tuhume-tuhume a kan mutanen da ake zargi, Mohammed Ali Abubakar da Celestina Emmanuel Yayock da Abdulbasit Adamu Sagagi da kuma Jazuli Kabir.
