Shugaban ECOWAS na ziyarar a Burkina Faso

Shugaban ƙungiyar ƙawancen tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afrika, ECOWAS, kuma shugaban ƙasar Saliyo, Julius Maada Bio, na wata ziyarar aiki a ƙasar Burkina Faso a ranar Talata.
Shugaba Bio na yunƙurin ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙungiyar ƙawance ƙasashen Sahel (AES) da ƙungiyar ta ECOWAS.
Ƙasashen na Sahel waɗanda ke ƙarƙashin mulkin soji, Burkina Faso da Mali da kuma Nijar sun ɓalle ne daga ECOWAS sannan suka kafa tasu ƙungiyar.
Manufar ziyarar shugaban ECOWAS ɗin shi ne, ƙarfafa dangantakar tsaro a yankin domin yaƙi da mayaƙa masu ikirarin jihadi da ke barazana ga yankin na Sahel.
