Ƙasashen duniya na mayar da martani kan harin Isra’ila a Qatar

0
1000147435
Spread the love

Harin da Isra’ila ta kai wa jagororin Hamas a babban birnin Qatar a wannan Talatar ya janyo caccaka daga sassan duniya, a yayin da magatakardan Majalisar Ɗinkin Duniya ya bayyana shi a matsayin ƙeta haddin Qatar a matsayin ƴantattar ƙasar.

Wannan ne hari na farko da Isra’ila ta kai Qatar, wadda ke a matsayin mai shiga tsakani a tattaunawar cimma tsagaita wuta tsakanin kIsra’ila da Hamas, kuma take ɗauke da sansanin sojin Amurka mafi girma a Gabas ta Tsakiya.

Magatakardan Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres ya bayyana hare-haren saman a matsayin ƙeta haddin Qatar a matsayinta ta ƙasa mai ‘yanci, kana ya ce dole ne dukkannin ɓangarorin su yi aiki tare don laluɓo zaman lafiya na ddindindin.

Shugaban Faransa Emmmanuel Macron, a wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, ya yi tir da harin, kana ya bayyana goyon bayansa ga Qatar, a yayin da gwamnatin Birtaniya ke cewa tana bibiyar lammuran da ke je ya zo, bayan da ta ce ba ta da masaniya akan harin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *