Mayaƙan ADF sun kashe mutane sama da 50 a gabashin Jamhuriyar Congo

Gungun mayaƙan tawaye na ƙungiyar ADF, ɗauke da muggan makamai sun afka wa wani taron binne gawa, inda suka kashe mutane sama da 50 a gabashin Jamhuriyar Congo.
Harin da ‘yan ta’addan na ADF suka kai da misalin ƙarfe 9 na daren jiya Litinin, a ƙauyen Ntoyo da ke garin Lubero a Lardin Arewacin Kivu, shi ne mafi girma da aka shaida a baya bayan nan.
Kanal Alain Kiwewa da ke riƙon ƙwaryar shugabancin garin na Lubero, ya ce kimanin mutane 60 mayaƙan na ADF masu alaƙa da IS suka kashe, kuma akwai yiwuwar adadin ya ƙaru la’akari da cewar har yanzu akwai mutanen da ake lalube bayan ɓacewar da suka yi.
Yayin na shi ƙarin bayanin wani jami’in gwamnati, Macaire Sivikunula, ya ce gungun ‘yan ta’addan sun yi amfani ne da adduna wajen sanadin salwantar rayukan akasarin mutanen da suka yi wa kisan gillar.
Ko a watan jiya, sai da ‘yan ta’addan na ADF suka kashe fararen hula fiye da 50 yayin wasu jerin hare-hare da suka kai, yayin da kuma a cikin watan Yuli suka halaka aƙalla mutane 38 a wani farmakin na dabam da suka kai kan wata Mujami’a.
Tuni dai hare-haren da mayaƙan ADF suka koma kai wa a Gabashin Jamhuriyar Congo ya sake dagula lamurra a yankin da ya sha fama da hare-haren ‘yan tawayen M23 da Rwanda ke marawa baya a faron shekarar nan.
