NCAA ta gayyaci kamfanonin jiragen saman cikin gida kan matsalar ɗage tashin jirage

Hukumar kula da jiragen sama ta Najeriya (NCAA) ta kira dukkanin kamfanonin jiragen sama na cikin gida taro a Abuja kan matsalar ɗage tashin jirage da mayar wa da fasinjoji kuɗaɗensu.
Mai magana da yawun NCAA, Michael Achimugu, ya ce taron zai gudana ranar Laraba a ofishin hukumar.
Wannan na zuwa ne kusan sa’o’i 24 bayan Achimugu ya ce hukumar tana da ikon da gwamnatin Tarayya ta ba ta “na fara bayyana sunaye da tona asirin kamfanonin jiragen sama da ke ɗage ko soke tashin jirage, musamman a lokutan da ba a saba ba, ba tare da samar da kwanciyar hankali ga fasinjojin da abin ya shafa ba kamar yadda sashe na 19 na dokokin jiragen sama na Najeriya ya tanada.
Ya bayyana cewa za a tattauna batutuwan da suka shafi ɗage tashiwar jirage, da halayen fasinjoji masu tada husuma da yadda ake mu’amala da su, da batutuwan mayar wa da fasinjoji kuɗi da biyan diyya da ajiye na’urar RFID wato wata ƙaramar na’ura da ke ajiye bayani kuma ana amfani da ita wajen sadarwa da sauran na’urori a cikin jaka da kuma hanyoyin kare ma’aikatan jirgi daga fasinjoji.
Ya kuma jaddada cewa bisa ƙa’ida, idan aka ɗage tashin jirgi tsakanin ƙarfe 10 na dare zuwa 4 na safe, dole a samar wa fasinjoji masauki.
Ya gargaɗi kamfanonin jirage da su daina barin fasinjoji cikin wahala tare da barin jami’an NCAA su fuskanci wulaƙanci.Achimugu ya ce: “Idan kuna son a kira ku kamfanonin jirage na duniya, ku inganta ayyukanku, don mutuncinku da kuma amincin fasinjoji.
