Habasha za ta ƙaddamar da tashar lantarki mafi girma a Afirka bayan shekara 14 ana aikinsa

Kasar Habasha za ta kaddamar da wani babban dam da aka gina a kan kogin Nilu bayan shafe shekaru goma sha hudu ana aikin.
Babbar madatsar ruwa ta Habasha, wacce za ta kasance tashar samar da wutar lantarki mafi girma a Afirka.
Tasha ce za ta riƙa samar da wuta mai karfin wutar lantarki fiye da megawatt 5000.
Aikin kogin dai ya haifar da rikicin diflomasiyya domin Sudan da Masar sun kasance suna adawa da aikin.
