Gwamnatin Tinubu ta kusa fara cin bashi daga Opay – Dino

0
1000145939
Spread the love

Tsohon ɗantakarar gwamnn jihar Kogi, Sanata Dino Melaye ya ce ganin yadda gwamnatin Najeriya a ƙarƙashin Bola Tinubu ke cin bashi, yana ganin gwamnatin za ta iya cin bashi daga kamfanin hada-hadar kuɗi na intanet wato Opay da moniepoint.

Dino ya bayana haka ne a zantawarsa da tashar ARISE a ranar Litinin, inda ya zargi gwamnatin da jefa ƴan ƙasar cikin mawuyacin hali ta hanyar ciyo basussuka da yawa, waɗanda ya ce ba a ganin amfanin su a ƙasa,

“Ana fama da yunwa sosai a ƙasar nan. Me ya sa shugaban ƙasa zai ciyo basin dala biliyan 1.7 daga bankin duniya? me ya sa majalisar dattawa ta amince da bashin dala biliyan 21 zuwa yanzu, sannan akwai wasu da ke tafe?”

Ya ƙara da zargin cewa “wannan gwamnatin ce wadda ta fi sakaci a tarihin Najeriya. Idan ana samun kuɗin shiga, me ya za kuma ake cin bashi. Ba za mu yi mamaki ba idan nan gaba kaɗan muka ga shugaban ƙasa ya fara cin bashi daga Opay da Moniepoint.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *