Hukumar NEDC ta kaddamar da wadansu ayyuka a Jahar Adamawa

Hukumar raya yankin arewa maso gabas ta shirya tura motocin dake amfani da lantarki, da bullo da shirin inshorar lafiya, da fadada ayyukan more rayuwa a jihar Adamawa a wani bangare na aikinta na maido da walwala, sake gina al’umma, da samar da ci gaba mai dorewa a yankin Arewa maso Gabas.
Da yake jawabi a Yola, Kodinetan Hukumar NEDC na Jiha, Khalifa Muhammad Lawan, ya ce Hukumar ta kudiri aniyar ganin kowane gida sun ci gajiyar ayyukan ta ta hanyar hada kai da masu ruwa da tsaki ciki har da kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ).
Ya bayyana cewa shirin na fitar da motocin lantarki da shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da su, zai hada da motocin bas na zirga-zirgar mutane, da motocin haya da za su iya daukar fasinjoji uku, da Keke Napep masu amfani da hasken rana da aka inganta don daukar fasinjoji har takwas.
Tun lokacin da aka kafa hukumar NEDC ta fara aiwatar da ayyuka da dama a Adamawa. Wadannan sun hada da gine-gine da gyara makarantu a dukkanin kananan hukumomi 21, da samar da kayan ajujuwa da kayan horar da sana’oi, da kafa manyan makarantu guda uku.
Haka kuma ta gina gidaje masu tarin yawa guda 500 a kananan hukumomi shida tare da gudanar da ayyukan hanyoyi a wasu yankuna.
