Jam’iyyar APC ta lashe amanta a Ganye

An dauke Motan da Jam’iyyar APC ta kawo da nufin gyaran hanyar Jada-Mbulo.
Yayin da aka rantsar da sabon zababben dan majalisan dokokin Jaha mai wakiltan mazabar Ganye Hon Misa Musa Jauro, jam’iyyar APC da ta sha alwashin gyaran hanyar Jada-Mbulo da ta dauki hankali a yayin zaben ta dauke motocin da ta kawo da nufin gyaran hanyar.
Da farko mutanen Ganye suna tunanin hakan zai faru, inda da dama ke ganin sun yi amfani da wannan daman wajen cin zabe ne kawai.
