NAFDAC ta gargaɗi mutane game da wasu jabun allurai a Najeriya

Hukumar kula da inganci da magunguna ta Najeriya, NAFDAC, ta gargaɗi ƴan ƙasar kan amfani da wasu allurai da ta ce ta gano jabu ne aka haɗa ana sayarwa a kasuwanni da kantunan magunguna a faɗin ƙasar, inda ta buƙaci mutane su kula.
NAFDAC ta bayyana haka ne a wata sanarwar gargaɗi da ta fitar a shafinta na X, inda ta bayyana cewa ba a yi wa alluran rajista da hukumarsu ba.
Ta ce akwai allurar Gold Vision Oxytocin mai ɗauke da lambar rajista NAFDAC ta bogi ta A4-9566, wadda ta ce ana haɗawa a kamfanin Anhui Hongye Pharmaceutical Co., Ltd da ke titin Fengyang ta Gabas a lardin Anhui da ke ƙasar China, amma kamfanin Gold Vision Medicals da ke titin Range Avenue a jihar Enugu ta kudancin Najeriya ke kasuwancinsa
