Gwamna Bago ya rusa majalisar zartarwa ta jihar Neja

Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya rusa majalisar zartaswar jihar, wanda ya kawo karshen wa’adin dukkanin kwamishinonin sa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a yayin zaman majalisar da aka gudanar a gidan gwamnati dake Minna.
Gwamna Bago ya nuna jin dadinsa ga ‘yan majalisar komishinonin sa masu barin gado bisa gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban jihar.
Ya umurci kwamishinonin da ke barin gado da su mika al’amura ga sakatarorin dindindin na ma’aikatunsu daban-daban.
Gwamna Bago ya yi nuni da cewa sakataren gwamnatin jiha (SSG), shugaban ma’aikata, mataimakin shugaban ma’aikata, da sauran manyan mukamai a ofishinsa za su ci gaba da kasancewa a kan mukamansu.
