Mutane sama dubu 23 ne suka ɓata a sassan Najeriya – Red Cross

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce sama da mutane 23,659 ne suka bace a Najeriya, inda iyalai 13,595 ke cikin kunci, yawancinsu mata dake kokawa da rashin tabbas.
Shugaban Kungiyar ta ICRC a Damaturu, Ishaku Luka, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin gudanar da bukukuwan tunawa da ranar mutanen da suka bace a duniya.
Ya ce kashi 68 cikin 100 na wadanda har yanzu ake neman su mata ne, yayin da kashi 59 cikin 100 na wadanda suka bata kananan yara ne a lokacin da suka bace.
A cewarsa, jihar Yobe kadai ce ke da mutane 2,500 da suka bace, wanda akasari aka samu a karamar hukumar Gujba. Ya bayyana cewa, batun bacewar mutanen na daya daga cikin mafi munin sakamakon tashe-tashen hankula, da bala’o’i, da ake fiskanta.
Ya kuma bukaci bangarorin da ke rikici da juna da hukumomi da al’umma da su kara taimakawa wajen hana bacewar mutane.
Luka ya kara da cewa kungiyar ta taimaka wajen hada yara bakwai da suka rabu da iyalansu.
