Girgizar kasa ta Afganistan ta kashe mutane fiye da 600 tare da jikkata wasu 1,500

Akalla mutane 600 ne suka mutu inda wasu 1,500 suka jikkata bayan wata girgizar kasa a gabashin Afghanistan.
Hukumar binciken yanayin kasa ta Amurka ta ce wata girgizar kasa mai karfin awo 6 ta afku da tsakar dare a gabashin Afghanistan da ke kusa da kan iyaka da Pakistan.
Gidajen da aka yi da laka da katako sun ruguje yayin da aka aike da jirage masu saukar ungulu don kwashe wadanda suka jikkata.
Akwai rahotannin da ke cewa an ji girgizar kasa a makwabciyarta Pakistan da kuma Indiya.
