An ƙone wata mata a Neja bisa zargin ɓatanci ga Annabi Muhammad

0
1000106026
Spread the love

Mutanen garin Kasuwar-Garba da ke ƙaramar hukumar Mariga ta jihar Neja sun ƙone wata mata da ranta a yammacin jiya Asabar bisa zarginta da ɓatanci ga Annabi Muhammad.

Matar, wadda ake kira da Amaye, tana sayar da abinci ne a yankin, inda jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wani kwastomanta ya yi mata magana cikin raha cewa yana so zai aure, sai ya ambato maganar Annabin, ita kuma a nan ta faɗa wata magana ta zama ɓatancin.

An ce an fara miƙa ta ofishin ƴansanda ne domin a gudanar da bincike, amma sai mutane suka ci ƙarfin jami’an tsaron, suka ƙwace ta, sannan suka cinna mata wuta.

Shugaban ƙaramar hukumar Mariga, Abbas Adamu Kasuwar-Garba ya tabbatar aukuwar lamarin, inda ya ce komai ya lafa zuwa yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *