Tsohon Shugaban ‘Yan Sandan Nijeriya Solomon Arase ya rasu

0
1000105570
Spread the love

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya, Solomon Arase ya rasu a asibitin Cedarcrest da ke Abuja.

Kawo yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance daga iyalansa ko rundunar ‘yan sandan Najeriya dangane da mutuwar sa.

An nada Arase, Sufeto-Janar na ‘Yan sandan Najeriya na 18 a watan Afrilun 2015 ta hannun Shugaba Goodluck Jonathan na lokacin.

Bayan ya yi ritaya a shekarar 2016, ya ci gaba da yi wa kasa hidima a bangarori daban-daban, musamman a matsayinsa na Shugaban Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda (PSC), rawar da ya taka har zuwa watan Janairun 2023 a karkashin Shugaba Muhammadu Buhari.

A watan Yunin 2024 ne Shugaba Bola Tinubu ya sauke shi daga mukamin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *