Wata mata ta hada baki da saurayi ta karbi kudin fansa N3m daga iyaye

0
1000103668
Spread the love

Wata mata ‘yar shekara 23 mai suna Nmesoma Josephine Nwoye, ta hada baki wajen boyewa da nufin cewa anyi garkuwa da ita domin karbar kudi daga hannun iyayenta.

Rahotanni sun bayyana cewa an yi garkuwa da ita ne tare da saurayin ta mai suna Chibuike Ogbu mai shekaru 24 wanda kariya ne suka shirya a tsakanin su.

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Anambra sun kama dukkanin wadanda ake zargin ne a ranar Juma’a, tare da kwato kudi naira miliyan 1.2 daga hannunsu a matsayin kudin fansa da iyayen yarinyar suka biya tun farko.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, SP Tochukwu Ikenga ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *