Akwai rawar da sarakuna zasu taka domin tabbatar da tsaron Jahar mu – Dikko Radda

Bayan munanan hare hare da yan bindiga suka kai karamar hukumar Malumfashi na Jahar Katsina a makon da ya gabata, Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda ya gana da Sarakunan Katsina Da Daura.

A yayin ganawar tasu a gidan Gomnati dake birnin Katsina Dikko Radda ya kara Jaddada Kudirinsa Na Magance Matsalar Tsaro A Fadin Jihar.

Jahar Katsina dai na cikin jahohin Najeriya dake fama da matsaloli na tsaro dake da alaka da ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Jahar na iyaka da Jahohin Zamfara, Kaduna, Kano da kuma Jamhuriyar Niger ta Arewacin ta.
