An daure wani basaraken Najeriya Joseph Oloyede bisa laifin zamba a Amurka

Bayan samun sa da laifi na zamba Oba Joseph Oloyede na Ipetumodu a jihar Osun, ya shiga gidan yari a Amurka.
Alkalin kotun, Christopher Boyko, ya yanke wa sarkin hukunci a ranar Talata kan badakalar dala miliyan 4.2.
Rahotanni sun bayyana cewa an kama Oba Oloyede da wani Fasto dan Najeriya, Edward Oluwasanmi a watan Afrilun 2024, sakamakon badakalan sama da dala miliyan 4.2 na COVID 19.
A cewar takardar tuhume-tuhume guda 13 da ake yi musu, mutanen din biyu sun gabatar da bukatar lamuni tare da bayanan karya.
Duk da haka, Mai shari’a Boyko a hukuncin da ya yanke a ranar Talata ya yanke wa Oloyede hukuncin zaman gidan yari na watanni 56, ya umarce shi da kuma ya biya $4,408,543 a matsayin diyya.
Ofishin lauyoyin Amurka da ke gundumar Ohio ta Arewa a cikin wata sanarwa da aka fitar, ya bayyana cewa Sarkin na Najeriya zai yi asarar dala 96,006 da masu bincike suka kama a baya da kuma gidansa na gundumar Medina.
A watan Yulin 2025 ne kuma kotun ta yanke wa Fasto Oluwasanmi hukuncin daurin watanni 27 a gidan yari.
