Mataimakin gwamnan jihar Taraba Alkali ya dawo bayan doguwar jinya

Mataimakin gwamnan jihar Taraba, Aminu Alkali ya koma Jalingo babban birnin jihar bayan ya kwashe tsawon lokaci yana jinya.
Rahotanni sun bayyana cewa Alkali ya taho ne ta filin jirgin Yalo.
Akwai kuma wani faifan bidiyo da ya yi ta zagayawa a shafukan sada zumunta dake nuna dawowar sa.
Alkalin ya taho ne daga Abuja kuma aka kai shi gidansa da ke gidan gwamnati a cikin ayarin motoci.
Aminu Alkali dai ya dawo ofis ne bayan watanni takwas da suka gabata, kuma tun a wancan lokacin ake ta rade-radin cewa Alkali yana fama da wata cuta da ba a bayyana ba.
