Hukumar IAEA ta sanar da shirin dawo da masu sa ido kan nukiliya a Iran

Shugaban hukumar kula da makamashin Nukiliya ta Majalisar Ɗinkin Duniya IAEA, Rafeak Grossi, ya ce tawagar masu sa ido kan nukiliya su koma Iran.
Grossi ya ce yanzu haka suna tattaunawa da gwamnatin Tehran domin cigaba da sa wa ayyukanta na nukiliya ido a cibiyoyinta.
Ya ce da zarran sun koma bakin aiki zasu tabbatar sun sanya ido domin tabbatar komai ya tafi bisa sharuɗɗaan da aka yarje.
Wannan shi ne karo na farko da hukumar ke koma wa bakin aiki a Iran tun bayan harin da Amurka ta kai wa cibiyoyin nukiliyar Iran a watan Yuni.
Iran dai ta dakatar da bai wa IAEA haɗin kai tun bayan wannan lokaci.
