An yi nasarar ku6utar da wani da akayi garkuwa dashi a Adamawa.

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa tare da hadin guiwar kwararrun ‘Yan sa kai, sun yi nasarar ceto wani da aka yi garkuwa da shi a ranar 25/08/2025, ba tare da samun rauni ba, bayan wani aikin hadin gwiwa da suka kai a yankin tsaunuka na karamar hukumar Gombi.
Labarin wannan nasarar dai na kunce ne a cikin wata sanarwan da kakakin rundunar ‘Yan Sandan Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ya fitar.
SP Nguroje ya bayyana cewa bisa sahihan bayanan sirri da aka samu dangane da ma6uyar Yan ta’adda hadaddiyar tawagar ‘yan sanda tare da ‘yan sa kai suka kai farmaki ga sansanin ‘yan bindigan inda da ganin tawagar, masu garkuwar sun bude wuta, lamarin da ya kai ga musayar wuta a tsakanin su inda ‘yan bindigan suka yi sake wanda suka kama, Isah Adamu mai shekaru 28, mazaunin garin Gurin a karamar hukumar Fufore.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Adamawa, CP Dankombo Morris, yayin da yake yabawa jami’an da suka gudanar da aikin, ya tabbatar wa da jama’a cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike domin cafke wadanda ake zargin ya kuma umurci sashin yaki da garkuwa da mutane na rundunar da su karbe lamarin tare da tabbatar da gudanar da sahihin bincike kan lamarin.
CP Morris ya kara da cewa rundunar zata ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaro da tsaron dukkan mazauna jihar.
