ECOWAS na shirin ƙaddamar da rundunar yaƙi da ta’addanci

0
1000094232
Spread the love

Ƙungiyar ƙasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS ta bayyana shirin kafa rundunar gaggawa mai ƙarfin mutum 260,000 don yaƙi da ta’addanci da tashe-tashen hankula a yankin.

Wannan shi ne mafi girman shirin tsaro da ƙungiyar ta yi a kwanakin baya-bayan nan.

An bayyana wannan ne a taron manyan hafsoshin sojojin asashen Afirka da aka gudanar a Abuja, wanda ya tattaro manyan jami’an soja da jakadu da masana harkar tsaro.

Kwamishinan ECOWAS na harkokin siyasa da zaman lafiya da tsaro, Abdel-Fattah Musah, wanda ya yi wannan sanarwa, ya ce rundunar da za a kafa za ta ƙara ƙarfin runduna ta mutum 5,000 da ke ƙarƙashin tsarin zaman lafiya da tsaro na Tarayyar Afirka sosai.

ECOWAS na neman kasafin kuɗi na dalar Amurka biliyan 2.5 a shekara don ƙaddamar da rundunar, yayin da ministocin tsaro da kuɗi za su gana ranar Juma’a don kammala shirye-shiryen.

Haka kuma, ECOWAS na ƙarfafa tsaron ruwa tare da sabbin cibiyoyin tsaro guda uku da hedkwata ta haɗin gwiwa a Abuja don yaƙi da laifuka kamar fashi da makami da safarar mutane da dai sauran su.

Wannan mataki na zuwa ne a lokacin da Africa ta Yamma ke fama da tashin hankali na masu iƙirarin jihadi da juyin mulkin soja, da rashin kwanciyar hankali na siyasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *