Tinubu ya isa Brazil domin ziyarar kwana biyu

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya isa birnin Brasilia da ke ƙasar Brazil domin ziyarar aiki ta kwana biyu a ƙasar daga birnin Los Angeles na Amurka, inda ya samu tarba daga manyan jami’an gwamnatin Najeriya da takwarorin su na Brazil a filin jirgin Brasilia.
Ana dai sa ran Tinubu da Shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Sailva za su tatttauna su biyu ƙadai, sannan daga baya su fito su gudanar da taron manema labarai daga baya.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya Bayo Onanuga ya fitar, ya ce akwai alaƙa mai kyau tsakanin Najeriya da Brazil, inda ya ce a watan Maris na 2025, ƙasashen biyu sun ƙulla yarjejeninyar inganta noma da kasuwanci da tsaro da makamashi da ilimi da ma’adinai.
