Mun kashe ‘yan Boko Haram 35, – Sojin saman Najeriya

0
1000090292
Spread the love

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce ta kashe mayaƙa masu iƙirarin jihadi fiye da 35 a wasu hare-hare da ta kai jiya Asabar a jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar.

Ta ce ta kai hare-haren ne a wurare huɗu da ke maƙwabtaka da ƙasar Kamaru bayan samun bayanan sirri da suka nuna cewa sun taru a wuraren.

A kwanan nan ƙungiyar Boko Haram da Iswap sun matsa ƙaimi wajen kai wa sojoji hare-hare a yankin.

Sanarwar da rundunar ta fitar ta ƙara da cewa dakarun sojin ƙasa sun tabbatar cewa “yanayi a yankin ya lafa”

A ranar Juma’a ma rundunar sojin ƙasar ta ce ta kashe wasu kwamandojin Boko Haram biyu da kuma mayaƙa 11 a jihar ta Borno bayan sun daƙile harin da suka yi niyyar kai wa sojoji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *