Japan za ta bai wa Najeriya rancen dala miliyan 190 don inganta lantarki

Ministan Lantarki a Najeriya ya ce Adebayo Adelabu ya ce gwamnatinsu na shirin karɓar rancen dala miliyan 190 daga Japan domin “inganta ɓangaren makamashi mai dorewa”.
Acewar wata sanarwa daga ma’aikatarsa a ranar Asabar, ministan ya bayyana haka ne yayin taron ƙasashen Afirka da Japan da ke gudana a birnin Yokohama.
Ma’aikatar ta ce tawagar wakilan Najeriya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta tattaunada kamfanoni a ɓangaren lantarki da makamashi.
Da yake magana yayin taron, Mista Adelabu ya ce hukumar Japan International Cooperation Agency (JICA) ce za ta bayar da lamunin, inda shirin zai samar da makamashi maras gurɓata muhalli ga yankunan da ba su fiya samun sa ba a Najeriya.
“Wannan ƙari ne kan dala miliyan 750 da Bankin Duniya ya ba mu ƙarƙashin shirin Mission 300 Compact da zai samar da makamashi mai ɗorewa da tabbatacciyar lantarki ga mutum miliyan 17 a Najeriya,” in ji sanarwar.
