Matakin Hukumar EFCC na bayyana Haske a matsayin wanda ake nema ya haifar da ayar tambaya

0
1000088740
Spread the love

 An bayyana matakin Hukuncin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta dauka a baya-bayan nan na bada sammacin kama Bashir Abdullahi Haske a matsayin haramtacciyar doka da kuma cin zarafi, musamman ma dangane da bukatar da ke gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, na kalubalantar sammacin kama shi da hukumar ta samu tun farko.

Kamar yadda bayanan kotun suka nuna, Haske ya ci gaba da nuna aniyar sa na ba EFCC hadin kai da hukumomin da abin ya shafa.

Ya mutunta gayyatar da Hukumar ta yi a watan Yuli kuma ya ci gaba da bin duk umarnin, gami da bayar da takaddun likita biyo bayan matsalolin lafiya a lokacin da ake tsare da shi.

Tuni dai tawagar lauyoyin sa ta garzaya kotu inda suka gabatar da bukatar korin karar daga kotun tare da ajiye sammacin, inda suka ce an same shi ne ta hanyar da bata dace ba da boye bayanan gaskiya, da kuma take hakkinsa da tsarin mulki ya ba shi na yin adalci.

Takardan kotun ya samu sa hannun Nkemakolam Okoro, da sauran tawagan lauyoyi sa Dr. M.O. Ubani, sun tabbatar da cewa wannan matakin cin zarafi ne ga umarnin kotu.

Umurnin da aka bayar a ranar 8 ga watan Agusta na musamman ne domin a kama shi, ba wai a bayyana cewa ana nemansa ba.

Aikin EFCC shi ne ta yi yunƙurin aiwatar da kame, kuma, idan bai yi nasara ba, ta kai rahoto ga kotu.

Ta hanyar ƙetare wannan aikin na doka, Hukumar ta yi aiki da rashin bin doka da kuma tauye ikon shari’a, musamman ganin cewa takardar da kanta tana ƙarƙashin ƙalubale na doka.

Masu lura da al’amura sun yi nuni da cewa wannan furuci na zalunci ne, batanci, don bata sunan Haske.

Matakin bai zama dole ba, ganin cewa ba a tuhume shi da aikata laifin ba, kuma ya sha nuna aniyar yin hadin gwiwa da masu binciken.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *