Mutum huɗu ne suka mutu a kifewar kwale-kwalen Sokoto – NEMA

Hukumar bayar da agaji ta gaggawa a Najeriya Nema ta ce mutum huɗu ne ta tabbatar sun rasu sakamakon kifewar kwale-kwale da ta auku a jihar Sokoto a farkon makon nan.
Cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, Nema ta ce ta gano ƙarin gawar mutum ɗaya. Jimillar mutanen da aka ceto sun kai 41, a cear Nema.
Ta ƙara da cewa hakan ya sa ta kawo ƙarshen aikin neman waɗanda suka tsira da kuma neman gawarwaki, wanda ta gudanar tare da sauran hukumomin da lamarin ya shafa.
Ziyarar bincike da jami’an hukumar suka kai ranar Alhamis a ƙauyukan Takuske, Kwakwazu, Bari, da Gamiha – wuraren da fasinjojin suka fito – ta sa sun gano cewa akwai ƙarin mutum 16 da suka tsira daga hatsarin.
Hatsarinya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata bayan kwale-kwalen ya kife a madatsar ruwa ta Goronyo da ke garin Kojiyo.
