NDLEA ta ce ta kama matashi da tabar wiwi ta miliyan 10 a Kano

0
1000088717
Spread the love

Hukumar NDLEA mai yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Najeriya ta ce ta kama wani matashi mai suna Umar Adamu-Umar ɗauke da tabar wiwi mai nauyin 9kg da ta kai darajar naira miliyan 10.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar a yau Asabar ta ce dakarunta sun kama matashin mai shekara 27 a jihar Kano ranar 6 ga watan Agusta.

Ta ƙara da cewa na kama shi ne a kan babbar hanyar Kano zuwa Zariya yana shirin safarar ƙunshi 19 na tabar daga Legas zuwa Kano.

“Matashin ya amsa cewa yana safarar miyagun ƙwayoyin, kuma da ma hukumar ta kwana biyu tana saka masa ido,” mai magana da yawun NDLEA Sadiq Muhammad-Maigatari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *