Adadin mutanen da suka mutu a Gidan Mantau ya zarce 50

Ana ci gaba da neman mutane masu rai ko kuma gawarwaki a cikin dazuka bayan samun mutane sama da 50 da suka mutu a sakamakon mummunan harin da ƴan ta’adda suka kai garin Mantau da ke ƙaramar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.
Bayan kai harin an tabbatar da cewa mutane sun tarwatsa cikin dazuka, yayin da wasu kuma suka gamu da ajalinsu a cikin dajin.
A halin da ake ciki, yanzu haka, al’ummar yankin na kira ga gwamnatocin jihar Katisna da kuma na tarayya da su kai musu ɗauki don taya su neman ƴan uwansu da rai ko kuma gawarwaki.
Bayanai sun nuna cewa har yanzu yankin na Gidan Mantau na ƙarƙashin barazanar ƴan ta’adda don haka akwai ƙarancin cikakkun bayanai kasancewar ba’a iya shiga ko fita.
Wasu daga cikin waɗanda suka tsira sun tabbatar da cewa an ɗauki tsahon sa’o’i kafin jami’an gwamnati su isa yankin, kuma basu ƙarasa ba suka tsaya a hanya saboda haɗarin da ke kan hanya, inda suka ɗan tattauna da iyayen garin da kuma masu riƙe da sarautun gargajiya.
Zuwa yanzu dai an tabbatar da samun gawarwakin mutane 55, sama da 35 alƙalman da hukumomi suka bayyana.
